Motoci biyu dake cike da shinkafar da gwamnatin tarayya ta bayar aka rabawa kungiyoyi 436 dake jihar Kaduna a ranar Laraba.
Buhuna 2,400 na shinkafa mai nauyin 25kg shi ne kungiyar Arewa Youth Forum da ta jagoranci sauran kungiyoyin wajen rabon ta rabawa kungiyoyin da suka amfana.
A wata tattaunawa da ƴan jaridu a wurin taron rabon tsohon shugaban ƙungiyar ta AYF wanda a yanzu shi ne shugaban kwamitin aminta tun ƙungiyar, Gambo Ibrahim Gujungu ya ce an miƙawa kungiyar ta su motocin shinkafar a ranar Talata.
Buhunan shinkafar tallafi ne daga gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar kuɗi domin ragewa mutane raɗaɗin wahalar da ƴan Najeriya suke fuskanta saboda matsin tattalin arziki.