Kungiyoyi 436 sun amfana da  tallafin shinkafar gwamnatin tarayya

Motoci biyu dake cike da shinkafar da gwamnatin tarayya ta bayar aka rabawa kungiyoyi 436 dake  jihar Kaduna a ranar Laraba.

Buhuna 2,400 na shinkafa mai nauyin 25kg shi ne kungiyar Arewa Youth Forum da ta jagoranci sauran kungiyoyin wajen rabon ta rabawa kungiyoyin da suka amfana.

A wata tattaunawa da ƴan jaridu a wurin taron rabon tsohon shugaban ƙungiyar ta AYF wanda a yanzu shi ne shugaban kwamitin aminta tun ƙungiyar, Gambo Ibrahim Gujungu ya ce an miƙawa  kungiyar ta su motocin shinkafar a ranar Talata.

Buhunan shinkafar tallafi ne daga gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar kuɗi domin ragewa mutane raɗaɗin wahalar da ƴan Najeriya suke fuskanta saboda matsin tattalin arziki.

More from this stream

Recomended