Jihohin Bauchi da Zamfara dai har yanzu ba su samu tirelolin shinkafar da gwamnatin tarayya ta yi alkawari ga daukacin jihohin ba a matsayin wani mataki na rage radadin rashin abinci da ake fama da shi.
Sai dai jihar Bayelsa ta karbi tirela 20 na shinkafar daga gwamnatin tarayya domin rabawa dukkanin kananan hukumomin jihar nan take.
Wani babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa ga gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, Mustafa Jafaru, ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin jihar ba ta karbi shinkafar ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.