Fasinjoji da dama ne aka bada rahoton an yi garkuwa da su bayan da ƴan fashin daji suka buɗe kan wata mota ƙirar bus a mahaɗar Bishini dake kusa da Katari ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.
Wani mazaunin Katari, Saleh Ibrahim ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 09:00 na daren ranar Litinin inda ƴan fashin daji suka fito daga cikin dai-dai kan wata kwana inda suka buɗe kan motar mai cin fasinjoji 18 da ta ɗauko su daga Abuja zuwa Kaduna.
Ƴan bindigar sun harbin tayar motar abun da ya tilastawa motar shiga cikin daji kana daga bisani suka tasa ƙeyar fasinjojin ya zuwa cikin daji.
Ya ƙara da cewa an kuma tasa ƙarin wasu fasinjojin daga wasu motoci biyu ya zuwa cikin daji.
Ya cigaba da cewa abun haushin shi ne wurin da lamarin ya faru ba shi da nisa da shingen binciken da sojoji suka saka.