A ranar Alhamis ne babbar kotun birnin tarayya Abuja ta hana tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, diyarsa Fatimah da sirikinsa Jalal Hamma fita kasar waje.
Mai shari’a Sylvanus Orji ya yanke hukuncin cewa ba za su bar kasar nan ba har sai an kammala shari’ar da suke yi ta zambatar naira biliyan 2.7.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ya gurfanar da su ne a ranar Alhamis a kan tuhume-tuhume shida da ke da alaka da zamba na N2.7bn.
An gurfanar da su ne tare da Al-Buraq Investment Ltd.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta yi zargin cewa Sirika ya ci zarafin ofishinsa ta hanyar ba da kwangilar N1.3bn ga kamfanin Nigerian Air Start-up to Tianero Nigeria Limited.