Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20.

Dan marigayin, Ibrahim Zakari, wanda ya yi wannan zargin, ya ce lamarin ya kai ga mutuwar mahaifinsa.

Ibrahim ya ce tashin hankalin ya fara ne a lokacin da mahaifinsa ya dawo daga kasuwa, matar sa Sadiya Salisu ta ce ta karbi gishirin naira 20 a matsayin bashi, matakin da ya fusata mahaifinsa wanda a baya ya yi gargadi game da karbar kowane irin lamuni daga kowa.

Ibrahim ya ce rigimar da ta faru tsakanin marigayin da matarsa ta kai ga yin musayar kalamai.

Dan ya ce mahaifinsa ya koma shagonsa ya kira kanen matarsa a waya ya shaida masa duk abin da ya faru a gida tsakaninsa da matarsa.

An yi zargin cewa daga nan ne dan uwan matar ya fusata ya zo gidan yana neman mijin ‘yar uwarsa amma bai same shi a gida ba, ya yanke shawarar binsa zuwa shagonsa da ke ‘Yan shinkafa a Kura.

Dan marigayin ya kara da cewa, nan take Magaji ya zubawa mahaifinsa ido, sai ya fara dukansa bayan da kashin kirjinsa ya karye.

Ya ce sun kai mahaifinsu wani asibiti da ke kusa da garin Kura inda wani likita ya yi masa magani ya sallame shi amma ya ce bayan sun koma gida mahaifinsa ya rasu, Ibrahim ya ce sun kai kara ofishin ‘yan sanda kuma jami’in ‘yan sanda na Kura ya gayyaci matar da dan uwanta yanzu haka suna hannun ‘yan sanda.

Ya yi kira ga kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano da ya tabbatar an yi wa mahaifinsa adalci.

More from this stream

Recomended