A yammacin ranar Talata ne shugaba Bola Tinubu ya isa Legas daga birnin Landan domin gudanar da bukukuwan sallar Eid-el-Kabir na ranar Laraba.
A Jirgin na Gulfstream Tinubu ya isa filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Ikeja da karfe 05:05 na yamma agogon kasar inda dimbin magoya bayansa suka tarbe shi.
Wannan ya kawo karshen ziyararsa ta mako guda a birnin Paris- inda ya halarci taron sabuwar yarjejeniya ta hada-hadar kudade ta duniya da shugaban Faransa Emmanuel Macron da kuma birnin Landan suka shirya, domin wata ziyara ta sirri.