Jami’an tsaron hukumar farin kaya ta DSS sun kama, Doyin Okupe tsohon darakta janar na yakin neman zaben Peter Obi.
A cewar lauyansa, Tolu Babaleye an kama dan siyasar ne a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa London.
A kwanakin baya ne wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta samu Okupe da hannu dumu-dumu a badakalar kudin makamai inda ta ci shi tarar miliyan 13 ko kuma zaman gidan yari.