Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya sauka a kasar Equatorial Guinea domin halartar taron shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Africa AU.
A cikin wani hoto da ya wallafa a shafinsa na Facebook, mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya ce Buhari na tare da matarsa, Aisha da kuma yayansa biyu a yayin ziyarar.