
Hakkin mallakar hoto
@Nasir Ahmad El-Rufai
Hadarin gas ya lakume rayuka tare da raunata wasu mutane a garin Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Mazauna yankin sun kadu matuka sakamakon bindigar da gas din ya yi wanda ya ritsa da adadin mutanen da hukumomi ba su bayyana ba tare da raunata wasu.
Wasu hotunan da jama’a suka yadawa a shafukan zumunta sun nuna irin barnar da lamarin ya yi.
A takarda mika ta’aziyya ga iyalan mamatan da wadanda suka samu rauni kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya yaba wa ‘yan kwanakwana da sauran hukumomi bisa matakan gaggawa da suka dauka bayan aukuwar lamarin.
Gwamantin jihar Kaduna ta bayyana alhininta game da mutuwar mutanen sakamakon fashewar gas din a harabar wani kamfani da ke a Unguwar Sabon tasha.
“Gwamnatin jihar Kaduna na mika ta’aziya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hadarin gas a yau. “Muna taya su alhinin wannan bala’i da ya faru.”
Shi ma da yake yin jaje game da gobarar gas din dan majalisar dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Sanata Uba Sani, ya yi addu’ar samu rahama ga mamatan. Dan majalisar ya ce mahukuntar jihar za su dauki matakan kare aukuwar irin haka a nan gaba.
“Ina jinjiya ga kokarin da ‘yan kwanakwanda da sauran jami’an tsaro suka yi wurin shawo kan lamarin.
Ina rokon Allah Ya yi wa mamatan rahama sannan ba wa wadanda suka samu rauna sauki.
Wadanda suka yi asara kuma kada su yanke kauna.”