YAYAN SHUGABA BUHARI NA SON A HADA SU DA JUNA

Rahoton Datti Assalafiy

Jama’a wannan bawan Allah da kuke gani a hoto sunansa Idi Usman, amma amfi saninsa da sunan Baba Idi, yanzu haka yana da zama a wani gari mai suna Garin-Gabas dake karamar hukumar Hadejia jihar Jigawa, yana da shekaru 95 a duniya.

Baba Idi jinin shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne, babansu daya da shugaba Muhammadu Buhari, Mahaifiya ce kowa da nasa, yana matsayin yaya ga shugaba Buhari

Yadda abin ya kasance shine: asalin Mahaifiyar Baba Idi ‘yar garin Garin-Gabas ce, shekaru kusan dari 100 da suka gabata mahaifinta ya dauketa suka tafi garin Daura karatun Allo, anan ne mahaifin su shugaban kasa Muhammadu Buhari wato Malam Usmanu ya ganta kuma ya aureta tare da mahaifiyar babbar yayan su shugaba Buhari ana kiranta da suna ‘Yar Dindi amma ta rasu.

Mahaifin su shugaba Buhari yana da mata biyu a lokacin kafin ya auro mahaifiyar shugaba Buhari kenan, sai aka samu cikin Baba Idi, anan ne aurenta da mahaifin su shugaba Buhari ya mutu ta koma garinsu Garin-Gabas a Kasar Hadejia tana dauke da cikin Baba Idi kenan.

Shi kuma mahaifin su shugaba Buhari wato Malam Usman sai ya sake yin wani aure, ya auri wacce ta haifi shugaba Buhari, shugaba Buhari bai shekara 4 ko 6 a duniya ba Mahaifin nasu Malam Usmanu ya rasu, Buhari sai ya tashi a hannun Mahaifiyarsa, lokacin ita kuma mahaifiyar Baba Idi ta jima da haifar Baba Idi a Garin-Gabas har ma ya girma ta kaishi makarantar Allo kafin mahaifiyar shugaba Buhari ta haifeshi a Daura

Kakan su shugaba Buhari wato wanda ya haifim Babansu ‘ya’yansa uku ne, akwai;

1- Usman wanda yake shine mahaifin su shugaba Buhari da Baba Idi )
2- Abdullahi
3- Sarki Muhammad Bashari (Baban Sarkin Daura na yanzu wanda shugaba Buhari yake amfani da sunansa

Baba Idi bai taba sanin mahaifinsa ba, tunda Mahaifiyarsa ta kaishi makarantar Allo bai dawo gida ba sai kamar bayan shekaru 35, ya zo ya tarar da mahaifiyarsa ta rasu a nan garin Garin-Gabas kenan, shine sai ya fadawa ‘yan uwan mahaifiyarsa cewa su kaishi gurin Mahaifinsa, ko kuma su fada masa inda mahaifinsa yake zai je, to shine sai aka fada masa cewa mahaifinka jinin Sarauta ne a Masarautar Daura, sunansa Usmanu yana garin Daura

A lokacin Baba Idi bai tafi Daura neman Mahaifinsa ba sai daga baya, yace min yanzu shekaru 47 da suka gabata ya fara zuwa garin Daura neman mahaifinsa, yaje ya tarar da Sarkin Daura na lokacin Marigayi Sarki Muhammadu Bashari (yayan babansu kenan wanda shugaba Buhari ke amfani da sunansa), ya musu bayani cewa shi ‘dan Usmanu ne, yazo neman mahaifinsa, to shine Sarkin Daura Muhammadu Bashari yace to ga gidan ubanku nan amma ya jima da rasuwa, ka zauna ka kwana, washegari zan hadaka da ‘yan uwanka na jini maza da mata, sai Baba Idi yace masa kafin nan, zan koma gida na taho da matata da ‘ya’ya na

Daga nan Baba Idi ya dawo gida Garin-Gabas, ya fadawa matarsa cewa ya samu labarin Mahaifi da ‘yan uwansa da gidansu na gado, ta shirya zasu koma gida Daura, shine sai matarsa taki amincewa, to daga nan Baba Idi bai sake komawa garin Daura ba tun bayan shekaru kusan 50 da suka gabata

Baba Idi yana da tabbacin cewa shugaba Buhari kaninsa ne da suke uba daya, shi ma shugaba Buhari ya san yana da yaya wanda ya tafi karatun Allo, amma bai taba saninsa ba, shugaba Buhari ya samu labarin yana da yaya ko dai a gurin Mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, ko kuma ya samu labarin a gurin marigayi Sarkin Daura Muhammadu Bashari, don tabbatar da haka; lokacin da shugaba Buhari yaci zaben 2015, bayan shekara biyu ko uku, akwai wata hanya da Buhari yaje ya kaddamar a wani gari mai suna Guri a Kirikasamma jihar Jigawa, to a wannan lokacin Buhari yayi magana akan cewa yana da yaya a Jigawa, sai dai shi kanshi bai sani ba ko yayan nasa yana raye

Duk da haka Baba Idi baiyi kasa a gwiwa ba, yana ta kokarin ganin ya samu haduwa da kaninsa shugaba Buhari, a wannan shekara da muke ciki (2019) Baba Idi yaje garin Daura har sau biyu, a gidan jikan shugaba Buhari yake sauka mai suna Buhari, a fadar Masarautar Daura sun masa tambayoyi yana basu amsa, sun tabbata shi ‘dan gidane, ance za’a hadashi da kaninsa shugaba Buhari, har suka dauki hotonsa da jininsa, suka bashi kudi Naira dubu 100,000, sai dai abin takaici Baba Idi ya tabbatar min da cewa ana boye wa shugaba Buhari batunsa

Ina da nambar wayanshi, duk lokacin da naga dama ina kiranshi mu tattauna, yace min bashi da wani buri a duniya illa ya hadu da kaninsa shugaba Buhari inyasu ya fadi ya mutu bukatarsa ta biya, jama’a ku duba idon Baba Idi da hakorinsa da tsayinsa da tsayuwarsa akwai alamar nasaba ta kamanni tsakaninsa da shugaba Buhari, har jinin jikinsa aka dauka don a hadashi da kaninsa amma ana boyewa

Don Allah jama’ar Musulmi, duk wanda yake da wata hanya da zai hada wannan bawan Allah da ‘dan uwansa shugaba Buhari ya taimaka yayi don Allah, tun daga kan Malaman addinin Musulunci, da ‘yan siyasa da masu tallafawa shugaba Buhari muna neman alfarma, don Allah kuyi sanadin haduwar wannan bawan Allah da shugaba Buhari don a bincika a tabbatar da cewa wannan yayan shugaban Kasa ne, babu shakka duk wanda yayi sanadin haduwarsu zai samu lada mai dunbin yawa a gurin Allah (T)

Ba zan fitar da nambar wayansa a cikin wannan sakon ba sai ta sirri, saboda gujewa makircin ‘yan damfara
Ina Malam Bashir Ahmad mai tallafawa shugaban kasa Buhari ta sabbin kafofin watsa labarai na yanar gizo?
Malam Bashir Ahmad na san zaka karanta wannan sakon, ban taba neman alfarma a gurinka ba amma yau ina nema, kayi amfani da damarka wajen isarwa shugaba Buhari sako da zai taimaka wajen haduwa da yayansa da suke uba daya don girman Allah.

Related Articles