Ƴan sanda sun kama wacce ta lakaɗa wa mahaifiyarta duka

Rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF), ta kama wata mata ‘yar jihar Anambra da ke yi wa mahaifiyarta tsohuwa duka.

An dauki hotonta ne a cikin wani faifan bidiyo tana dukan mahaifiyarta mai shekaru da dama tare da watsa mata bokitin ruwa.

Kakakin rundunar ƴan sanda a Jihar Anambra, Ikenga Tochukwu, ya tabbatar wa manema labarai damke matar a ranar Lahadi.

Tochukwu ya bayyana cewa wanda ake zargin ta yi wa mahaifiyarta mai shekaru 75 bulala.

Ya ce: “An kama wanda ake zargin da yi wa tsohuwa bulala a kai a kai tare da watsa mata ruwa a kwance a kasa, an kama ta kuma an tsare ta domin gurfanar da ita.”

More from this stream

Recomended

Trump Ya Yaba Wa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan abin da ya bayyana a matsayin ƙwazon jagorancinsa wajen yaƙi da ta’addanci da magance matsalar tsaro a ƙasar. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Trump ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Tinubu. Ya ce yana yaba wa shugaban […]