Ƙungiyar Yan’uwa Musulmi ta Najeriya wacce aka fi sani da shi’a ta yi zargin cewa mambobin ta huɗu jami’an ƴan sanda suka kashe a Kaduna a ranar Juma’a.
Da yake magana da ƴan jaridu bayan yamutsin da ya faru, Aliyu Tirmizy ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar ya ce an kuma jikkata ƙarin wasu mutanen 20.
Tirmizy ya ce suna gudanar da zanga-zanga ne domin nuna goyon baya ga al’ummar Falasɗinawa amma sai ƴan sanda suka tarwatsa su.
“Yawanci muna fitowa a kowace Juma’a ta ƙarshen watan Azumin Ramadana domin yin zanga-zangar lumana ta nuna goyon baya ga Falasɗinawa kamar yadda ake a sauran sassan duniya kan yadda ake musguna masu,” ya ce.
“Yawanci muna zanga-zangar cikin lumana amma a wannan karon muna shirin farawa sai ƴan sanda suka zo suka fara harba barkonon tsohuwa da kuma harbi inda suka kashe mambobin mu huɗu tare da jikkata wasu 20.”ya ce
Amma kuma mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kaduna,Mansir Hassan ya ce babu wanda aka kashe ya ƙara da cewa ba ayi amfani da harsashi ba wajen tarwatsa masu zanga-zangar.