Zargin satar rogo ya sa wani uba ya kashe ɗansa

Boniface Innocent Uko mahaifin wani matashi mai shekaru 26 ya sassara dan nasa da adda har lahira bayan da ya girbe gonar rogonsa ba tare da saninsa ba.

Da yake mayar da martanin kan zargin kashe dan nasa Mr Innocent Uko wanda dan asalin kauyen Ebe Ikpe ne a karamar hukumar Essein Udem ta jihar Akwa Ibom ya ce haushin girbe rogon ba tare da izininsa ba ne yasa ya kashe ɗan nasa.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, SP Odiko Macdon ya bayyana jaridar Daily Trust cewa bayan kashe dan nasa mutumin ya kona gawar tare da boye ta acikin wani ramin masai da ba a amfani da shi.

More from this stream

Recomended