Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta tura ƴan sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta.
Kamar yadda masu shirya zanga-zangar suka faɗa za a fara jerin gwano na tsawon kwanaki 10 daga ranar 1 ga watan Agusta.
A wata sanarwa ranar Juma’a, Josephine Adeh mai magana da yawun rundunar yan sandan birnin ta ce an jibge jami’an tsaron ne domin tsaron lafiyar jama’a, ta masu zanga-zanga da kuma hana ɓata gari shiga zanga-zangar.
Adeh ta ce Benneth Igweh kwamishinan ƴan sandan birnin ya tabbatarwa da mazauna birnin cewa jami’ansa za su kare rayuka da dukiya baza kuma su lamunci aikata ɓarna ba.
Ta shawarci mazauna birnin da su kai rahoton duk wani motsi da basu yarda da shi ba.