Yanayin tsaro a Nijar na cigaba da tabarbarewa bayan da yan bindiga su ka kashe sojoji 7

Yanayin tsaro a Jamhuriyar Nijar na cigaba da daukar wani salo mara daɗi inda ya yake cigaba da tabarbarewa duba da yadda ake cigaba da samun karuwar hare-hare daga yan ta’adda.

Hakan na zuwa ne bayan da yan ta’ada suka a sake kai hari kan sojojin kasar.

Wannan ne dai hari na hudu da aka kai kan sojojin kasar tumbayan juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasa, Mohamed Bazoum.

Harin na baya_bayan nan an kai shi ne a yankin Tillaberi inda yan ta’addar suka kashe sojoji 7 tare da yin awon gaba da makamai masu yawan gaske.

More from this stream

Recomended