Yan sanda sun kama mutane uku da ke shirin sace daliban sakandare a Kebbi – AREWA News

Rundunar yan sandan jihar Kebbi ta kama wasu mutane uku da ake zargi da shirya yin garkuwa da daliban makarantar sakandaren fasaha ta gwamnatin tarayya dake Zuru.

Yayin da yakewa yan jaridu jawabi kwamishinan yan sandan jihar, Garba Danjuma ya ce mutane ukun da ake zargi da shirin yin garkuwa da daliban sun fito ne daga jihar Kebbi.

Ya ce tunda fari sun rubutawa shugaban makarantar wasika kan shirinsu na kai hari makarantar tare da sace dukkanin dalibanta.

Kwamishinan ya ce wani mai suna,Sani Shehu da kuma dansa, Muhammad A. sani daga jihar Yobe sune aka kama kan shirya harin.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...