Wasu ganau kuma mazauna kauyen na Gidan Kaso, wadanda su ka bukaci a sakaya sunayensu saboda tsoron abin da ka biyo baya, sun ce maharan sun isa garin ne da babura kuma sabe da bindigogi da yammacin jiya Asabar su ka shiga bude wuta da kuma kone-kone. Su ka ce kusan duk wayewar gari sai wadannan maharan sun far ma wasu mutane a yankin. Su ka ce saboda yawan kai hare-haren da mutanen ke yi, har manoman yankin sun kasa zuwa gonakinsu duk kuwa da damina ta kankama.
‘Yan yankin su ka ce idan ma an girke sojoji a Birnin Magaji, kamar yadda hukumomi ke ikirari, to girke sun bai yi wani tasiri ba – a kalla ya zuwa yanzu dai. Haka ma jiragen sintirin da ke tauna tsakuwa a yankin; sun ce bas u hana miyagun cin karansu ba babbaka.
Duk wani kokari na jin ta bakin ‘yan sanda ya ci tura.