Wani mutum ya mutu a cikin masallaci a Abuja

An gano gawar wani matashi da aka bayyana da suna Rayyanu  a wani masallaci bayan sallar asuba a garin Paso dake ƙaramar hukumar Gwagwalada a birnin tarayya Abuja.

Wani mazaunin Paso, Ibrahim Musa ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata wajejen ƙarfe 05:56 na safe lokacin da marigayi Rayyanu yaje masallacin domin yin sallar asuba.

Ya ce marigayin yaje masallacin akan babur inda ya yanke shawarar yin bacci bayan salla amma ya mutu a cikin baccinsa.

”  Wajejen ƙarfe 07:28 lokacin da wasu mutane dake da alhakin share masallacin suka ga mutum a kwance a cikin masallaci. Sun yi ƙoƙarin tashinsa su share wurin amma baya motsi,” a cewar Musa

Ya ce mutanen sun jawo hankalin mutane kan halin da ake ciki abun da ya jawo hankalin wasu dattawan Musulmai dake yankin wanda suka garzaya wurin suka ɗauke shi ya zuwa asibiti inda likitan dake bakin aiki ya tabbatar da mutuwarsa.

More from this stream

Recomended