Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya yi wata tattaunawa mai muhimmanci da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, kan rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine.
A cikin wani rubutu da ya wallafa a Truth Social, Trump ya ce sun amince da “tsagaita wuta nan take kan duk wasu gine-gine da kayayyakin makamashi.”
Haka nan, shugabannin biyu sun cimma matsaya kan yin gaggawar kammala yarjejeniyar tsagaita wuta gaba daya domin kawo karshen wannan yaki mai muni.
Trump ya kara da cewa, “Wannan yaki ba zai taba faruwa ba in da ni ne shugaban kasa tun farko!”
Ya ce an tattauna hanyoyin kulla yarjejeniyar zaman lafiya, inda ya bayyana cewa Putin da Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine na bukatar kawo karshen rikicin.
“A halin yanzu, an fara aiwatar da wannan tsari, kuma da fatan alheri, domin jin dadin bil’adama, za mu cimma nasara!” in ji Trump.
Trump da Putin Sun Cimma Yarjejeniya Kan Tsagaita Wuta a Yakin Rasha da Ukraine
