Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya tashi daga filin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja ya zuwa kasar Faransa.
Ajuri Ngelele mai magana da yawun shugaban kasar shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Laraba.
Ngelele wanda bai yi karin haske ba kan makasudin tafiyar shugaban kasar ya fadi cewa shugaban kasar zai dawo gida Najeriya a makon farko na cikin watan Faburairu.
Wannan ne karo na farko da shugaban kasar yake fita kasar waje tun bayan da ya bada umarnin daukar matakin rage kashe kuɗi da ya ƙunshi rage kaso 60 na tawagar dake masa rakiya.