Tinubu Ya Gana da Hafsoshin Tsaro, Akpabio da Wasu Manyan Jami’ai a Fadar Shugaban Kasa

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaro a fadarsa da ke Abuja a ranar Talata.

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ne ya jagoranci tawagar hafsoshin.

Babu cikakken bayani kan dalilin taron, amma ana kyautata zaton yana da nasaba da matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a sassan kasar, musamman hare-haren da ake zargin kaiwa a Jihar Benue da wasu yankuna.

Taron ya samu halartar mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, babban sifeton ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, da Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta DSS, Oluwatosin Ajayi.

Haka nan, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da jagoran masu rinjayen majalisar, Opeyemi Bamidele, sun halarci zaman. Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da mataimakinsa, Ben Kalu, su ma an hangosu a wajen taron.

Ana sa ran bayan taron, gwamnati za ta fitar da matakan da za a dauka domin magance matsalar tsaro da sauran muhimman batutuwan da suka shafi kasa.

More from this stream

Recomended