Tarihin hawa da saukar farashin man fetur daga 1973 zuwa 2020 a Najeriya | BBC Hausa

man fetur

A ranar Laraba 2 ga watan Satumban 2020 ne ƙungiyar masu gidajen mai masu zaman kansu ta Najeriya IPMAN, ta umarci ‘ya’yanta su ƙara kuɗin farashin mai zuwa Naira 162 kan kowace lita.

Ipman ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamakon karin kudin mai da gwamantin Najeriya ta yi zuwa N151.56k.

Tun bayan hawan shugaba Muhammadu Buhari karagar mulkin Najeriya, an yi ta samun ƙarin kudin man fetur a lokutan daban-dana, kamar dai yadda ya sha faruwa a gwamnatocin baya.

Duk da cewa ba wannan ne karo na farko da aka taɓa yin ƙarin farashin mai a ƙasar ba, hakan ya tayar da hankalin mutane da dama.

BBC ta yi nazari kan tarihin ƙarin farashin mai da shugabannin da suka gabata suka sha yi a ƙasar, tun daga 1973 lokacin mulkin Janar Yakubu Gowon zuwa yau.

Bayanan hoto,
Janar Yakubu Gowon ne shugaban kasa na farko da ya fara kara farashin man fetur

A 1973, Janar Yakubu Gowon ya ƙara farashin man fetur wanda a iya cewa shi ne na farko, daga kobo shida zuwa kobo takwas da rabi, wato kashi 40.8 cikin 100 kenan a kan kowace lita.

A 1976, Janar Murtala Muhammad ya ƙara farashin man daga kobo takwas da rabi zuwa kobo tara, wato da kashi 0.59% kan kowace lita.

Ranar 1 ga watan Oktobar 1978 ne Janar Olusegun Obasanjo ya ƙara farashin daga kobo tara zuwa kobo 15.3, wato kashi 70 cikin 100 kan kowace lita.

20 ga watan Afrilun 1982, Alhaji Shehu Shagari ya sake ƙara farashin daga kobo 15.2 zuwa kobo 20, wato kashi 30.71 cikin 100, a kan lita guda.

A ranar 31 ga watan Maris na 1986 kuma Janar Ibrahim Babangida ya sake ƙara farashin daga kobo 20 zuwa kobo 39.5, kashi 97.5 cikin 100 kan kowace lita.

Janar Babangida ya sake ƙara farashin a ranar 10 ga watan Afrilun 1988, daga kobo 39.5 zuwa kobo 42, kashi 6.33 kenan cikin 100 kan kowace lita.

A ranar 1 ga watan Janairun 1989, Janar Babangida ya sake ƙara farashin daga kobo 42 zuwa kobo 60 ga motocin da ba na gwamnati ba.

Ranar 19 ga watan Disambar 1989 ya mayar da farashin na kowa da kowa.

Janar Babangida ya sake ƙara farashin daga kobo 60 zuwa kobo 70 a ranar 6 ga watan Maris 1991. Wannan ƙari ya zamo da kashi 16.67 cikin 100.

Shugaban riƙon ƙwarya Chif Ernest Shonekan shi ma ya yi wannan ƙarin farashi ranar 8 ga watan Nuwambar 1993, daga kobo 70 zuwa naira biyar, ƙarin da ya zama da kashi 614%.

Bayanan hoto,
Shugabannin kasar Najeriya da suka kara farashin man fetur a lokutan mulkinsu

A ranar 22 ga watan Nuwambar 1993 ne Janar Sani Abacha ya rage farashin man daga naira biyar zuwa naira uku da kobo 25, ragin kashi 35 cikin 100 kenan kan kowace lita.

Ranar 2 ga watan Oktobar 1994 kuma Janar Abachan ya ƙara farashin daga naira uku da kobo 25 zuwa naira 15, ƙarin kashi 361.54%.

A ranar 4 ga watan Oktobar 1994 Abacha ya sake rage farashin man daga naira 15 zuwa naira 11, ragin kashi 26.67%.

Shi ma Janar AbdusSalam Abubakar ya ƙara farashin daga naira 11 zuwa naira 25, ƙarin kashi 127.27%, a ranar 20 ga watan Disambar 1998.

A watan Janairun 1999 kuma ya rage farashin daga naira 25 zuwa naira 20.

Cif Olusegun Obasanjo ya ƙara farashin man daga naira 20 zuwa naira 30 a ranar 1 ga watan Yunin 2000.

A ranar 8 ga watan Yunin 2000 Obasanjo ya rage farashin daga naira 30 zuwa naira 22, ragin kashi 10 cikin 100.

Obasanjo ya sake ƙara farashin daga naira 22 zuwa naira 26 ranar 1 ga watan Janairun 2002.

Bayanan hoto,
Cif Olusegun Obasanjo ya kara farashin mai kusan sau biyar a zamanin mulkinsa

A watan Yuni 2003 Obasanjo ya sake ƙara farashin daga naira 26 zuwa naira 42.

Ranar 29 ga watan Mayun 2004 kuma chif Obasanjo ya mayar da farashin man naira 50. Ƙarin kashi 19.05%.

Ranar 25 ga watan Agustan 2004 ya sake ƙara farashin zuwa naira 65.

Ƙarin farashin mai na ƙarshe da Obasanjo ya yi shi ne ranar 27 ga watan Mayun 2007, inda man ya koma naira 75, ƙarin kashi 15.38%.

Shugaba Umaru Musa ‘Yar aduwa ya rage farashin mai daga naira 75 zuwa 65 a watan Yunin 2007.

Umaru ‘Yar Aduwa ne kadai wanda bai ƙara farashin man fetur ba cikin shugabannin da suka mulki Najeriya tun daga 1973.

A ranar 1 ga watan Janairun 2012 Goodluck Jonathan ya yi ƙoƙarin ƙara farashin zuwa tsakanin naira 138 da naira 250, amma daga bisani ya tsaya a kan naira 97.

Bayanan hoto,
An yi zanga-zangar nuna adawa da janye tallafin da Jonathan ya so yi

A watan Janairun 2015 kuma Shugaba Jonathan ya rage farashin daga naira 97 zuwa naira 87.

Ƙarin farashin mai a mulkin Buhari

Karin farashin mai na farko da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi shi ne ba da damar sayar da man a kan naira 87 da kobo 50 a gidan man ‘yan kasuwa ko da yake farashin bai sauya ba a gidajen man NNPC.

Tun daga wannan lokaci ba a sake samun ƙarin farashin man ba sai a ranar Laraba 11 ga watan Mayun 2016 da gwamnatin Shugaba Buhari ta mayar da shi naira 145.

A watan Maris 2020 – faɗuwar darajar fetur a kasuwar duniya ta sake tilastawa gwamnatin rage kudin man daga N145 zuwa N125.

Bayan wata guda, a karo na biyu a watan Mayun 2020, hukumar ƙayyade firashin albarkatun man fetur ta PPPRA ta sanar da sabon farashi daga N121.50 zuwa N123.50 lita guda.

Sai kuma a ranar Laraba 2 ga watan Satumban 2020 da ƙungiyar masu gidajen mai masu zaman kansu ta Najeriya IPMAN, ta umarci ‘ya’yanta su ƙara kuɗin farashin mai zuwa Naira 162 kan kowace lita.

Karin ya biyo bayan sanarwar da hukumomin Najeriya suka yi na kara kudin mai zuwa N151.56k.

Dogaro da man fetur – Sharhi da aka yi a 2016

Najeriya ƙasa ce da Allah ya albarkace ta da arziƙin man fetur, wanda kuma da shi ne ta dogara wajen samun kuɗin shigarta.

Sai dai duk da irin wannan ɗumbin arziƙin mai da Najeriya ke da shi, bai sa ƙasar ta wadatar da al’ummarta da man ba, ta yadda hakan ke jefa mutane cikin halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi a lokuta da dama.

Za a iya danganta hakan da rashin ingantattun matatun mai da ƙasar ba ta da su, ta yadda sai dai bayan ta sayar da ɗanyen manta ga wasu ƙasashen duniya, sai kuma ta koma wajensu ta sayo tattaccen man da za a yi amfani da shi.

Hakan ya sa take sayo man da tsada, dalilin da ya sa gwamnati biyan tallafin rarar man fetur ta yadda ‘yan ƙasa ba za su saya da tsada sosai ba.

Gwamnatin baya ta Goodluck Jonathan ta yi yunƙurin janye tallafin man, amma sai aka dinga zanga-zangar nuna adawa da wannan mataki.

Hangen masana tattalin arziki kan janye tallafin man fetur a 2016

  • Masana tattalin arziƙi sun yi ammanar cewa janye tallafin man fetur na da amfani da kuma rashinsa. Sai dai da yawa sun ce amfaninsa na dogon zango ne.
  • Masanan sun ce a halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki a yanzu, gwamnati ba ta da kuɗaɗen da za ta tallafa wajen biyan rarar.
  • Haka kuma ana iya amfani da makuɗan kuɗaɗen da ake kashewa wajen biyan tallafi a yi wasu ayyukan raya ƙasa da suke da muhimmanci sosai.
  • Za a samu gasa tsakanin manyan ‘yan kasuwa inda za su dinga karyar da farashin man, domin tsoron kada wani ya fi su samun tagomashi a harkar, kamar dai irin abin da ya faru a ɓangaren kamfanonin sadarwa.
  • Akwai hasashen cewa man zai wadata sosai a ko ina da kuma tabbacin daina samun dogayen layuka a gidajen mai.
  • Duba da halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki a yanzu da irin wahalhalun da mutane ke fuskanta, wasu na ganin janye tallafin man ba zai yi wa al’umma daɗi ba, musamman talakawa.
  • Farashin kuɗin abin hawa da na kayan masarufi zai ƙara hawa.
  • Zai bai wa ‘yan kasuwar man damar sanya farashi son ransu, ta yadda man zai fi farashin da gwamnati ta ƙayyade tsada.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...