Sojojin Sun Kashe Ɗan Ƙungiyar ISWAP A Jihar Borno

Sojojin rundunar tsaro ta Operation Haɗin Kai da aka ajiye a Miringa sun samu nasarar kashe wani mayaƙin ƙungiyar ƴan ta’addar ISWAP lokacin da suka daƙile wani farmaki da aka kawo musu.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ranar 24 ga watan Faburairu inda gamayyar sojojin runduna ta 231 da 331 dake aiki a makarantar Command Science Girls Secondary School dake ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno suka fuskanci hare-hare daga wasu ƴan bindiga dake kan babura.

Sojojin sun yi nasarar daƙile harin har ta kai ga sun kashe mutum guda daga cikin ƴan ta’addar.

Sojojin sun gano bindiga ƙirar PKT da kuma harsashi da da dama.

More from this stream

Recomended