Hereditar tsaron Najeriya ta bayyana cewa, dakarun Operation Delta Safe sun kama mutane 49 da ake zargi da hannu a satar mai tare da lalata masana’antun tace danyen mai haramtattu guda 22 a cikin mako guda.
Mai magana da yawun rundunar, Manjo Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan a rahoton mako-mako na ayyukan da dakarun sojin Najeriya ke gudanarwa a fadin ƙasar.
A cewarsa, sojojin sun hana satar man da darajarsa ta kai kimanin naira biliyan 869.2 a cikin makon.
Kangye ya ce cikin kayayyakin da aka kwato akwai lita 325,990 na danyen mai da aka sace, lita 24,645 na man gas (AGO) da aka tace ba bisa ka’ida ba, lita 19,500 na fetur (PMS), da kuma lita 1,600 na man injina.
Ya ƙara da cewa an kuma gano da lalata injinan sarrafa man haramtattu 86, rijiyoyin hakar mai 181, jiragen ruwa 25, babban jirgi mai saurin tafiya 1, tankokin ajiya 18, ganguna 316 da kuma gidajen tace mai haramtattu 22.
“Baya ga haka, an kwato janareto, na’urar tura ruwa, bututun ƙarfe, injin hako mai, babura, kekunan hawa uku, wayoyin hannu da motoci 18,” in ji shi.
Manjo Janar Kangye ya jaddada cewa rundunar soji tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro na ci gaba da nuna jarunta da kwarewa wajen tunkarar barazanar tsaro a sassan ƙasar.
Sojojin Najeriya sun lalata masana’antun sarrafa danyen mai haramtattu 22
