Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar Endbadgovernance sun gana da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.
A jiya ne shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya bawa ministan shari’a umarni janye dukkanin tuhumar da ake musu a gaban kotu.
Bayan hakan ne a yau ranar 5 ga watan Nuwamba gkotu ta sallame su tare da wanke su daga dukkanin zargin da ake musu ciki har da zargin cin amanar ƙasa.
Mataimakin shugaban kasar ya gana da yaran ne a madadin shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu.
Bayan ganawar da yaran ne mataimakin shugaban ƙasar ya damƙa su hannun gwamnonin jihohin Kano da Kaduna inda wasu daga cikin yaran suka fito.