Fasinjoji 21 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu jiragen ruwa suka ci karo da juna a Imore dake karamar hukumar Amuwo-Odofin ta jihar Lagos..
Jiragen da kowanensu ke ɗauke da mutane 16 sun ci karo da juna inda suka nutse a tsakiyar ruwa ranar Litinin da daddare.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin ya ce an kai rahoton faruwar lamarin ofishin ƴan sanda na Ilashe dake Jihar.
Ya ce fasinjoji 11 aka samu nasarar ceto wa lokacin da ake gudanar da aikin ceto a yayin da 21 suka nutse a ruwa.
Har kawo yanzu hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos, LASEMA bata fitar da wata sanarwa ba kan faruwar lamarin.