Matasa sun ƙona ofishin INEC a Benue

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa INEC ta ce an ƙona ofishin hukumar dake yankin Sankara a ƙaramar hukumar Ukum ta jihar Benue.

A wata sanarwa ranar Laraba, Sam Olumekun kwamishinan hukumar na sadarwa da kuma wayar da kan masu kaɗa riƙa ya ce Sam Egwu  kwamishinan zaɓe na jihar ne ya bayyana haka.

Ya ce matasan  yankin dake gudanar da zanga-zanga kan matsalar ƴan fashin daji a yankin su ne su farma ofishin hukumar da kuma wasu ofisoshin gwamnati da ƙarfe biyu na rana.

Sanarwar ta ƙara de cewa duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba amma an samu asarar kayayyaki ofisoshi da kuma na aikin zaɓe.

More News

An gano gawarwakin ƴan fashin daji 8 a Kaduna

Gawarwaki 8 da ake zargin na ƴan fashin daji ne aka gano bayan da sojoji suka kai farmaki dazukan dake ƙauyen Kurutu dake kusa...

Tinubu ya karɓi Anyim Pius a jam’iyar APC

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi wa  tsohon shugaban majalisar dattawa,Anyim Pius Anyim maraba da zuwa  jam'iyar APC. A makon daya gabata ne Anyim...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...