Matar aure yar shekara 15 ta sakawa mijinta shinkafar bera

Rundunar yansandan jihar Kano ta kama wata mata aure mai suna Hassana Lawal yar shekara 15 dake kauyen Beci a karamar hukumar Kumbotso ta jihar.

Ana dai zargin matar ne da sakawa mijinta,mai suna Sale Abubakar dan shekara 33 guba a abinci.

Mai magana da yawun rundunar yansandan jihar,DSP Abdullahi Haruna Kiyawa shine ya tabbatar da kamen cikin wata sanarwa da ya fitar.

Haruna ya ce ranar 16 ga watan Afirilu da misalin karfe biyu na rana rundunar ta samu rahoton dake cewa matar da ake zargi ta bawa mijinta abinci da shinkafar bera a ciki.

An dauki mutumin ya zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad domin samun kulawa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ya ce tuni suka kaddamar da bincike kan lamarin kuma za a gurfanar da wacce ake zargi gaban kotu da zarar an kammala binciken.

More News

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...

Hukumar NDLEA ta lalata sama da tan 300 na miyagun kwayoyi da aka kama a Legas da Ogun

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta yi nasarar lalata kilogiram 304,436 da lita 40,042 na haramtattun abubuwa da...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...