Malaman da suka je addu’ar buɗe gidan Bobrisky ba sa tsoron Allah—Sheikh Muyiddeen Bello

Wani malamin addinin Muslunci a Najeriya, Sheikh Muyiddeen Bello, ya soki lamarin wasu da aka ce Malaman Musulunci ne kuma suka je gidan ɗandaudu Bobrisky da sunan yi masa addu’ar buɗewa.

Malamin ya yi sukar ne cikin wata hira da ya yi da jaridar Punch.

A cikin hirar, an tambaye shi, ko Musulunci ya haramta sauya jinsi. Sai ya ce ai Musulunci ya haramta irin wannan ɗabi’a saboda ya hana Musulmi ya yi shiga irin ta mata ko Musulma ya yi shiga irin ta maza.

Bidiyon yadda wadancan malaman suka je gidan na Bobrisky ya karaɗe kafafen sada zumunta na zamani, inda mutane mutane da yawa suke Allah -wadai da hakan.

More News

Wasu gwamnoni tsofaffi da sababbi sun ziyarci Buhari a Daura

Wasu daga cikin sabbin gwamnoni da suka kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu da kuma wasu da suka sauka a ranar sun...

Hoto:Kwankwaso Ya kaddamar da wasu ayyuka a Kaduna

Biyo bayan gayyatar da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya yi masa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya kaddamar da wasu...

Sarkin Kano Aminu Ado ya zama uba ga Jami’ar Calabar

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya samu girmamawa bayan an nada shi a matsayin uban Jami'ar Calabar da ke Jihar Cross...