Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta ki tantance wani a matsayin kwamishina saboda rubutu a Facebook

Yayin zamanta na yau domin tantance sabbin Kwamishinoni, majalissar dokokin jihar Kaduna ta ki tantance Alhaji Aliyu Jaafaru a matsayin sabon Kwamishinan Noma Na jihar da gwamna Mallam Nasiru El-Rufai ya bada sunansa saboda wani rubutu dayayi na sukar Gwamnatin Jihar Kaduna akan tsarin tantance malaman makaranta da Gwamnatin tayi a shekarar 2017.

Alhaji Aliyu Jaafaru yazo zauren majalissar tun kafin shugaban majalissar ya iso, sai dai kuma bai samu tantancewa ba bayan da shugaban majalissar Alhaji Aminu Shagali yayi masa tuni akan rubun sukar Gwamnatin Jihar Kaduna dayayi a shekarar 2017 akan tsarin tsaftace Ilimi.

Shagali yace “A rubutunka da kayi a kafar sadarwar Facebook a shekarar 2017 ka soki Gwamnatinmu a bainar Jama’a inda ka bayyana Gwamnatinmu bamaison cigan jihar Kaduna bace”.

Shagali ya kara da cewa kayi rubutu kala-kala akan yunkurin Gwamnatin mu na tsaftace Ilimi”.

Daga karshe Shagali yadan bayyanawa Alhaji Jaafaru Irin rubutun da yayi a wancan lokacin inda yaki bada umarnin tantanceshi saboda rubutun dayayi a wancan lokacin.

Daga yake karin haske akan lamarin shugaban kwamitin majalissar akan harkokin sadarwa da yada labarai Alhaji Tanimu Musa ya bayyanawa manema labarai cewa anki tantance Alhaji Aliyu Jaafaru saboda ya kalubalanci Gwamnatin Mallam Nasiru El-Rufai a kafar Facebook a shekarar 2017.

Daga cikin kwamishinonin da aka tantance akwai Kwamishinan Tsare-tsare Mr Thomas Gyang, kwamishinan Fadar Gwamnati da Gyare-gyare Hassan Mahmud, sai mai binciken kudi Alhaji Atiku Musa inda majalissar ta bukaci daya fara binciken asusun kananan hukumomi nan take sai matemakiyar Gwamna a matsayin mukaddashin Kwamishiniyar Lafiya.

ZTH

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...