Magoya bayan Ambode sun gudanar da zanga-zangar lumana

Magoya bayan gwamnan jihar Lagos, Akinwumi Ambode sun gudanar da wata zanga-zangar lumana domin nuna goyonsu kan takarar gwamnan a karo na biyu.

Masu zanga-zanga sun dage kan cewa dole ne jam’iyar APC ta bawa kowanne dan takara dama a zaben fidda gwanin gwamnan da za a gudanar ranar Litinin.

Magoya bayan gwamnan sun yi jerin gwano tun daga Maryland ya zuwa Freedom Park dake Ojota.

Takarar gwamna Ambode a karo na biyu na fuskantar adawa daga wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyar da suke zargin gwamnan ya yi watsi da su.

Tsohon gwamnan jihar Lagos kuma jagoran jam’iyar APC na kasa, Bola Ahmad Tinubu na daga cikin na gaba-gaba wajen nuna adawa da takarar gwamnan.

More News

NDLEA ta kama wata Æ´ar Æ™asar Kanada da ta shigo da  ganyen tabar wiwi Najeriya

Jami'an hukumar NDLEA dake yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi sun kama, Adrienne Munju wata ƴar ƙasar Kanada da ta shigo da...

Yadda wani ango ya kashe tare da banka wa amaryarsa wuta har lahira

Ana zargin wani mai suna Motunrayo Olaniyi ya daba wa sabuwar amaryar sa, Olajumoke wuka har lahira, bayan wata zazzafar muhawara a gidan Amazing...

An ƙona ofishin hukumar zaɓen jihar Akwa Ibom

Wasu ɓatagari da ake kyautata zaton ƴan bangar siyasa ne sun ƙona ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Akwa Ibom dake ƙaramar...

An kwaso ƴan Najeriya 180 daga ƙasar Libiya

Ofishin hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA a jihar Lagos ya ce sun karɓi ƴan Najeriya 180 da aka dawo da su gida...