Maɓarnacin kayan wutar lantarki ya tsallake rijiya da baya a Jigawa

Wani matashi dan shekara 21 da ake zargi da yin barna a taransifoma mai suna Timothy Marcus ya tsallake rijiya da baya a jihar Jigawa.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata a unguwar Shagari da ke Dutse, babban birnin jihar, bayan da mazauna garin suka ga wanda ake zargin yana kokarin fitar da na’urar sulke daga taransifoma.

Kakakin hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC a jihar Jigawa, CSC. Adamu Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce da misalin karfe 1330 na safe hukumar NSCDC ta samu rahoton cewa wani da ake zargin barawon kayan wutar lantarkin ne ya shiga hannun mutanen unguwar Shagari inda suka yi masa mugun duka.

More from this stream

Recomended