Kotun Daukaka Kara Ta Jaddada Hukuncin Kisa Da Aka Yankewa Maryam Sanda 

VOA Hausa

A farkon shekarar nan babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yankewa Maryam hukuncin kisa bayan da ta same ta da laifin kashe mijinta Bilyaminu Bello, da ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP a Najeriya.

Alkalan kotun uku da suka saurari shari’ar, sun ce hujjojin da Maryam ta gabatar na kare kanta ba su da tushe balle makama.

Ita dai wacce ake tuhumar, wacce suke da ‘ya’ya biyu da marigayin, ta ce Bilyaminu ya fada ne akan madaukin shisha abin da ya yi sanadin mutuwarsa.

Lamarin ya faru ne shekarar 2017 bayan da ma’auratan suka samu sabani a tsakaninsu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito lauyoyin Maryam suna cewa za su daukaka kara zuwa kotun kolin kasar.

More from this stream

Recomended

Mutane 7 Sun Rasa Rqyukansu, 53 Sun Jikkata Sakamakon Guguwar Iska a Jigawa

Akalla mutane bakwai sun rasa rayukansu, yayin da 53 suka jikkata bayan wata guguwar iska ta yi barna a kananan hukumomi 13 na jihar Jigawa. Rahotanni sun nuna cewa guguwar ta shafi gidaje 5,403 a cikin garuruwa 120, inda ta lalata makarantu sama da 47, asibitoci uku, ofisoshin ‘yan sanda biyu, gidajen zama da sauran […]