Kotu za ta yanke hukunci kan rikicin APC a Kano.

A yau Talata ne ake sa ran Kotun Ɗaukaka Ƙara za ta yi zaman sauraron ƙarar rikicin shugabanci a jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kano tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau.

Ɓangaren Gwamna Ganduje ne ya ɗaukaka ƙarar bayan ya sha kaye a shari’o’i biyu da suka gabata, inda yake neman a soke shugabancin Ahmadu Haruna Zago, wanda ke samun goyon bayan tsohon Gwamna Shekaru, sannan a bayyana Abdullahi Abbas a matsayin halastaccen shugaba.

A wata shari’ar ta kotun tarayya na baya, kotun ta bayyana cewa ɓangaren Ganduje ba shi da hurumin neman a kori ƙarar saboda ya riga ya ɗaukaka ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara, saboda haka ne kuma ta yi watsi da buƙatarsu.

Rikicin APC a Kano ya samo asali ne tun bayan gudanar da tarukan jam’iyyar a matakin mazaɓu da jiha, abin da ya haddasa aiwatar da taruka biyu ƙarƙashin Sanata Ibrahim Shekarau da kuma ɓangaren gwamnatin Kano.

More from this stream

Recomended

Trump Ya Yaba Wa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan abin da ya bayyana a matsayin ƙwazon jagorancinsa wajen yaƙi da ta’addanci da magance matsalar tsaro a ƙasar. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Trump ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Tinubu. Ya ce yana yaba wa shugaban […]