Kotu ta soke zaben gwamnan jihar Osun

Kotun sauraran kararrakin zaɓen gwamnan jihar Osun ta soke nasarar da dan takarar jam’iyyar PDP kuma gwamna mai ci Ademola Adeleke ya samu a zaɓen gwamnan jihar.

A cikin watan Agusta ne tsohon gwamnan jihar, Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC ya shigar da kara gaban kotun inda yake kalubalantar nasarar da Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya samu.

Da yake karanta hukunci kotun a ranar Juma’a biyu daga cikin uku na alkalan kotu sun gamsu cewa mai kara ya tabbatar da zargin da yake cewa an samu kaɗa kuri’a ba bisa ka’ida ba a wasu tashoshin zaɓe.

More from this stream

Recomended