Jihar Yobe ta sanar da ranar yin zaɓen ƙananan hukumomi

Gwamnatin jihar Yobe ta ce ta shirya gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar 25 ga watan Nuwamba 2023.

Sakataren gwamnatin Jihar, Baba Mallam Wali shi ne ya bayyana haka cikin wata wasika da ya aikewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Jihar Yobe.

Wali ya aike da wasikar ne biyo bayan amincewar da gwamnan jihar, Mai Mala Buni ya yi na gudanar da zaben.

Gwamna Buni ya rushe shugabancin ƙananan hukumomin jihar biyo bayan karewar wa’adinsu.

More from this stream

Recomended

Trump Ya Yaba Wa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan abin da ya bayyana a matsayin ƙwazon jagorancinsa wajen yaƙi da ta’addanci da magance matsalar tsaro a ƙasar. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Trump ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Tinubu. Ya ce yana yaba wa shugaban […]