Hukumomin Ƙasar Masar Sun Bawa Daliban Najeriya Damar Shiga Kasar Daga Sudan

Abike Dabiri-Erewa shugaban hukumar NIDCOM dake lura da yan Najeriya mazauna kasashen waje ta ce gwamnatin Misra ta buÉ—e kan iyakarta ga É—aliban Najeriya da aka dauko daga Sudan.

Dabiri-Erewa ta ce an buÉ—e kan iyakar ne biyo bayan wayar tarho da shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi da takwaransa na Masar, Abdulfatah El-Sisi.

Sanarwar ta NIDCOM na zuwa ne sa’o’i bayan sanarwar da hukumar ta fitar dake cewa hukumomin Æ™asar Masar sun gaza buÉ—e kan iyakar duk da cewa jiragen rundunar sojan saman Najeriya sun isa kasar domin kwato É—aliban.

Ta kara da cewa an bude kan iyakar ne bayan gindaya wasu tsauraran sharuÉ—a da bata bayyana ba.

More News

Gwamnatin Adamawa Ta Ƙara Hutun Ɗaliban Makarantu Saboda Annobar Cutar Ƙyanda

Gwamnatin jihar Adamawa ta tsawaita lokacin komawar É—aliban jihar makarantunsu domin fara  zangon karatu na uku saboda annobar cutar Æ™yanda. A wata sanarwa ranar Litinin,...

Sojan Jamhuriyar Nijar sun kama Gawurtaccen ÆŠan Fashin dajin Najeriya Kachalla Mai Daji

Dakarun sojan Jamhuriyar Nijar sun samu nasara kama gawurtaccen É—an fashin dajin nan mai suna Kachalla Mai Daji a garin Illela dake kan iyakar...

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...