Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin daukar ma’aikatan koyarwa 3,500 a kwalejojin hadin kan gwamnatin tarayya a fadin kasar nan.
Dokta Yusuf Sununu, karamin ministan ilimi ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki na kasa kan manyan makarantun gaba da sakandare a Najeriya na kwanaki biyu.
Taron ya tattaro masu ruwa da tsaki a harkar ilimi domin tattauna kalubalen da ke fuskantar ilimin sakandare a kasar.
Taron dai an yi shi ne kan maudu’in, “Farfado da manyan makarantun Sakandare a Najeriya domin samun gogayya a duniya”.
Malam Sununu ya bayyana cewa daukar wadannan malamai zai inganta harkar ilimi sosai.