Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayyana shirinsa na sake fasalin tsarin zaben kananan hukumomin jihar domin samar da dama ga mutanen ‘masu gaskiya’ su tsaya takara.
Gwamnan ya bayyana haka ne a garin Mafa da ke karamar hukumar Mafa a jihar Borno a ranar Asabar, inda ya kara da cewa gyaran tsarin zai tabbatar da cewa masu kada kuri’a za su zabi mafi kyawun abin da suke so.
Zulum ya kada kuri’a a mazabar Ajari II mai lamba 006 a Mafa Ward, hedkwatar karamar hukumar.
Ya ci gaba da cewa, “Dole ne a inganta tsarin zabenmu, sannan a yi adalci sannan kuma muna bukatar masu gaskiya su tsaya takara, sannan muna son masu kada kuri’a da za su iya bambantawa, masu kada kuri’a za su iya zabar mafi inganci ba tare da son rai ba.”