

Gawar Marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ta iso Najeriya.
Sanarwar isowar gawar Najeriya na kunshe ne cikin wani sako da, Richard Olatunde tsohon mai magana da yawun gwamnan ya wallafa a shafin X inda ya ce gawar ta iso Najeriya da misalin karfe 03:39 na ranar Juma’a.
An kawo gawar gwamnan ne Najeriya daga kasar Jamus.
Matarsa Betty Anyanwu Akeredolu da ƴaƴansa da kuma yan uwa inda kaninsa mai binsa, Farfesa Wole Akeredolu ya jagorance su.