Fiye da dalibai 100 aka sace daga makarantar Islamiyya | Labarai

Maharan sun afaka cikin garin na Tegina ne a kan babura dauke da manyan bindigogi inda suka rinka harbe-harbe da ya kidima daukacin alummar garin, kafin suka yi wa makarantar ta Islamiyyar diran mikiya inda suka kwashe daliban. Rundunar ‘yan sandan jihar ta Neja, ta ce har yanzu ba su tantance adadin yaran da aka kwashe ba. Yayin da gwamnatin jihar ke bayyana takaicin sake fuskantar sace daliban makaranta.
Rahotani sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun bar wasu daliban saboda yara kanana ne da ba su iya tafiya sosai ba. Tuni dai gamaiyyar kungiyoyin farar hula na yankin arewacin Najeriya suka maida murtani a kan lamarin da suka bayyana shi da mai tada hankali. Yayin
Yawan sace daliban makaranta dai sannu a hankali ya zama ruwan dare, domin koda a watan Febrairun da ya gabata, sai da aka sace dalibai da malamai kimanin arba’in da daya a makarantar Sakandaren Kagara da ke jihar ta Neja, abinda ke nuna tabarbarewar yanayin tsaron da gwamnati ke cewa tana daukan matakin shawo kansa.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...