Birtaniya za ta taimaka wa Najeriya wajen yaki da ta’addanci | BBC Hausa

UK

Hakkin mallakar hoto
UK in Nigeria

Kasar Birtaniya ta yi alkawarin taimaka wa Najeriya wajen yaki da ayyukan ta’addanci a fadin kasar.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, Jeremy Hunt, ne ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyara yankin arewa maso gabashin Najeriya ranar Alhamis.

Hakazalika ya nanata bukatar neman sakin mutanen da kungiyar Boko Haram da kuma kungiyar IS suka sace a yankin Yammacin Afirka.

Mista Hunt ya kuma kai ziyara cibiyar ajiye abinci ta hukumar abinci ta duniya wato World Food Programme a birnin Maiduguri, inda ya gana da ma’aikatan hukumar wadanda suke samar da abinci ga ‘yan gudun hijira.

Ya kuma gana da wata rundunar sojin Birtaniya, wadda take bai wa sojojin Najeriya horo.

Birtaniya tana taimaka wa Najeriya a fannin tsaro da ayyukan jin kai da kuma ci gaban al’umma.

Har ila yau, kasar ta bai wa sojojin Najeriya kimanin 30,000 horo a ‘yan shekarun nan.

A matsayinta na kasa ta biyu wadda ta fi ba da tallafi a fannin ayyukan jin kai, kasar ta kashe fam miliyan 300 a tsawon shekara biyar.

Kuma tana kokarin magance tushen abin da ke jawo rikici, inda kasar take taimakon Najeriya wajen samar wa al’ummarta ingantaccen ilimi da bunkasa harkokin kiwon lafiya.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...