
Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta koma ta biyu a Premier League, bayan cin Leeds United 2-0 a wasan mako na 23 ranar Lahadi.
Marcus Rashford ya fara cin kwallo a minti na 80, kuma na 13 da ya zura a raga tun bayan kammala gasar kofin duniya.
Ba dan wasan da ya kai Rashford yawan zura kwallaye a raga tun bayan da aka kammala gasar kofin duniya a Qatar a 2022.
Sauran minti biyar a tashi daga wasan a Elland Road, United ta kara na biyu ta hannun Alejandro Garnacho, wanda hakan ya sa ta hada maki uku.
United ta ci kwallo biyu amma ba a karba ba, har da wadda Rashford ya kara a raga.
Da wannan sakamakon United ta koma mataki na biyu a teburin Premier League da maki 46.
Manchester City za ta karbi bakuncin Aston Villa a Etihad a wasan mako na 23 a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Lahadi.
City, mai rike da Premier na bara tana ta uku da maki 45 a teburin bana.
Golan Manchester United, David de Gea ya yi wasa na 400 a Premier League, shine na farko da ba dan Birtaniya ba da ya yi wannan bajintar.
Ranar Laraba United da Leeds suka tashi 2-2 a kwantan wasan Premier League mako na takwas a Old Trafford.
United ta ci wasa na shida a waje a bana kenan, wadda a bara ma fafatawa shida ta yi nasara a karawar da ta kai ziyara a bara.
Kuma a wasa biyar da ci a bana a waje, duk da 1-0 ta yi nasara.