
Asalin hoton, Getty Images
Cin zarafin da ake yi wa dan wasan Real Madrid, Vinicius Junior matsala ce gabaki dayan kwallon Sifaniya in ji Carlo Ancelotti.
Sau uku ana cin zarafin dan wasan Brazil, mai shekara 22 a kakar bana a Sifaniya.
An dauki bidiyon magoya bayan Mallorca a lokacin da suke kalaman cin zarafin dan wasan a karawar da aka ci Real 1-0 ranar Lahadi.
”Ban san dalilin da ake cin zarafin Vinicius ba, ya kamata a magance matsalar, ”in ji Ancelotti.
A watan Satumba wasu magoya bayan Atletico Madrid sun rera wakar cin zarafin Vinicius, lamarain da kungiyar ta yi tur da aka aikata.
A watan Disamba, Vinicius ya fada cewar ya kamata La Liga ta kawo karshen kalaman cin zarafi da magoya baya ke yi a wasan da Real ta ci Valladolid 2-0.
A watan jiya an yi wani butun-butumin Vinicius, wanda aka rataye a kusa da wata gada a filin atisayen Real Madrid. ‘Yan sanda na binciken lamarin.
Neymar da wasu fitattu a fannin tamaula sun goyi bayan Vinicius a watan Satumba, bayan da wasu ke alakanta rawar da yake idan ya ci kwallo da biri.
Vinicius ya yi bidiyo, inda ya ce ba zai taba daina rawa ba idan ya ci kwallo, rawa ce ta bakaken fatar geBrazil da suke yi a lokacin annashuwa.