Sanata Aleiro ya bude sabon ofishin APC a Kebbi

Rikicin shugabanci a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya ya ƙara ƙamari, bayan da tsohon gwamnan jihar Sanata Muhammadu Adamu Aleiro ya buɗe wata sabuwar hedikwatar jam’iyyar ta jihar a ranar Lahadi.

Hakan kuwa na faruwa ne duk da ƙoƙarin sasanta rikicin da ke tsakanin ɓangarensa da na gwamnan jihar, Sanata Atiku Bagudu da kwamitin Abdullahi Adamu ya yi.

Bangaren Gwamna Bagudu dai ya bayyana buɗe sabon ofishin a zaman haramtacce wanda aka yi ba bisa doka ba.

Wasu na ganin wannan matakin na Sanata Aleiro a matsayin wanda zai iya janyo wa jihar ta Kebbi tashin hankalin siyasa, wanda a baya ake yi wa jihar kallon cewa ba a cika samu ba.

Amma bude ofishin bai gudana kamar yadda aka tsara da farko ba saboda yayin isa wajen taron, an tarar da jami’an tsaro bila adadin cikin shiri domin hanawa.

Sanin abin da ke iya faruwa idan suka nace sai sun bude ofishin, sai tsohon gwamnan tare da dandazon magoya bayansa ciki har Alhaji Bello Bagudu yayan Gwamna Atiku Bagudu, suka karkata akala zuwa filin Sukuwa inda suka yi taron buɗe ofishin.

Bayanan hoto,Wannan kuma ita ce hedikwatar APC mai biyayya ga Gwamna Bagudu

An bude ofishin ne a gidan jigon APC Alhaji Bello Bagudu wan Gwamna Atiku Bagudu.

Sai dai a halin yanzu ko tsuntsu babu a ciki saboda jami,an ba su bari a je ko kusa da ita.

Alhaji Sani Dododo shi ne kakakin ɓangare Sanata Aleiro, kuma ya bayyana wa BBC cewa babban dalilin samun wannan rabuwar kan yana da nasaba da wani taron APC da aka yi a baya inda aka cimma matsaya daban-daban, wanda ba a cimma ba kamar yadda aka zauna aka tsara.

Sai dai kakakin jam’iyyar bangaren Gwamna Atiku Bagudu, Alhaji Isa Assalafi ya nace kan cewar jam’iyyar ba ta rabu ba kamar yadda ake faɗa.

“Jam’iyyar APC a Kebbi na nan tare, tsintsiya ce maɗaurinta daya.”

Ga alama dai har yanzu da sauran kallo domin kowane ɓangare ya miƙa wa hukumar zaben jihar sunayen ƴan takaransu a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar da kansiloli da za a yi ran biyar ga watan Fabrairu.

Bayanan hoto,Wannan kuma ita ce hedikwatar APC mai biyayya ga Gwamna Bagudu

More News

Buhari ya kai ziyara Equatorial Guinea

Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya sauka a kasar Equatorial Guinea domin halartar taron shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Africa AU. A cikin wani hoto da ya...

Zulum wins Borno APC ticket, rejects offers to be VP in 2023

Borno State Governor Babagana Zulum has won the All Progressives Congress (APC) ticket to run again in 2023. Zulum will face Mohammed Ali Jajari of...

Amaechi’s ally, Tonye Cole wins APC governorship primaries in Rivers

Business mogul, Tonye Cole, has emerged winner of the All Progressives Congress, APC, governorship primaries in Rivers State. Cole is said to be the preferred...

Jigawa APC primaries: Fear God, vote wisely – Guber aspirant, Aliyu tells delegates

One of the gubernatorial aspirants of the All Progressives Congress (APC) in Jigawa State and former member of the House of Representatives, representing Buji/Birnin...