Ba so muke mu balle daga Najeriya ba – Nnamdi Kanu

Jagoran kungiyar IPOB a Najeriya Mr. Nnamdi Kanu, dake neman kafa jamhuriyar Biafra, dan gwagwarmaya kuma wanda aka sako a ‘yan kwanakin baya daga gidan yari bayan da hukumomin Najeriya suka zarge shi da laifin cin amanar kasa da neman tada zaune tsaye, ya bayyanawa Muryar Amurka cewa “ba so suke su balle daga kasar ba amma dai suna so ne su koma kamar yadda suke kafin zuwan turawan mulkin mallaka.”

A wata hira ta musamman da yayi da wakilin muryar Amurka, Peter Clottey, wanda ya tambaye shi ko yana gani hukumomin Najeriya zasu amince da yinkurin ballewar wani yanki a kasar, Nnamdi Kanu ya ce abu ne mai yiwuwa saboda a cewar sa, duk wata kasa da ake mulkin kama karya kamar Najeriya zata iya kin amincewa da wannan matakin, “amma kuma abinda suka manta shine su suka fara kawo rarrabuwa a kasar, su kuma ne suka soma kawo nuna bambanci da son kai, kuma suke tafiyar da harkokin kasar kamar wata harkar iyali.

Nnmadi Kanu, wanda ya ziyarci Muryar Amurka, ya kara da cewa ba zasu nade hannuwansu su zuba ido suna ganin abinda ke faruwa ba. Ya kuma ce ba zasu kara barin tarihi ya sake maimaita kansa ba, kamar abinda ya faru a shekarar aluf dari tara da sittin da shida lokacin da aka kashe dubban ‘yan kabilar Igbo a arewacin kasar.

Sai dai kuma za’a tuna cewa kisan da wani rukunin soja ‘yan asalin kabilar Igbo suka yi wa manyan shugabannin Arewa da suka hada da Frayim-ministan Nigeria Abubakar Tafawa Balewa da Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello, shine babban dalilin da ya haddasa wannan yakin da Nigeria ta abka a cikinsa a wancan lokacin.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...