Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Borno, ta lashe dukkan kujerun shugabanni 27 da na kansiloli 312 a zaben kananan hukumomin jihar Borno da aka gudanar a ranar Asabar.
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Borno, BOSIEC, Lawan Maina ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana sakamakon zaben da aka gudanar ranar Lahadi a Maiduguri.
“Bayan gudanar da zaben a ranar Asabar, a yau mun samu sakamako daga kananan hukumomi 27 kuma kamar yadda doka ta ba mu a sashe na 10.”
A matsayina na babban jami’in zaben jihar, zan karanta sakamakon kamar haka:
“Jam’iyya mai mulki, APC ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomin jihar 27.”
Haka kuma, jam’iyya mai mulki ta lashe dukkan kansiloli (kansiloli) 312 a daukacin kananan hukumomin jihar.
“Da wannan ne muka kawo karshen wannan aikk kuma za a gabatar da takardar shaida ga wadanda suka yi nasara a wani lokaci da za a bayyana nan ba da jimawa ba,” in ji Maina.