An sace ‘sama da mutum 100’ masu ibada a wani coci a Kaduna

Elrufai

Asalin hoton, Kaduna Govt

Bayanan hoto,
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce tana kan tattara wasu bayanai game da sabbin hare-haren da aka ƙara kai wa bayan na cocin kafin ta fitar da sanarwa gaba ɗaya

Ćłan bindiga sun sace sama da mutum 100 da hallaka mutum guda da kuma jikata wasu biyu a wani hari da suka kai wani coci a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, a cewar shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar, Rabaran Joseph John Hayab.

Rabaran Hayab ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a Cocin Emanuel Baptist da ke ƙauyen Kakkaudaji a wajen garin Kaduna a ranar Lahadi, yayin da mutane ke tsaka da yin ibada.
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa tana kan tattara wasu bayanai game da sabbin hare-haren da aka ƙara kai wa bayan na cocin kafin ta fitar da sanarwa gaba ɗaya.
Bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da mabiyan ke tsakiyar ibada a cikin cocin nasu, inda suka suka abka musu ta harbe-harbe.

A baya ‘yan bindigar sun tarwasta tare da fattakar al’ummar yankin Ć™auyen Kakkaudaji wanda ke kusa da Unguwan Ayaba, suka kuma mamaye shi bayan wani mummunan hari da suka kai.

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya a jihar ta Kaduna ta nuna rashin jin dadinta game da yadda ake yawan kai hare-hare tare da sace-sacen jama’a don neman kudin fansa a jihar, duk kuwa da matakan da gwamnatin jihar ke cewa tana dauka.
“Jiya ana cikin sujjada sai Ć´an bibdiga suka shigo Ć™auyen, da farko sun je cocin yara ne daga baya suka sauya ra’ayi suka tafi na manya. A nan ne suka harbe mutum É—aya ya mutu a take har ma an yi jana’izarsa jiya.
“WaÉ—anda suka ji rauni kuma suna asibiti a Kaduna. SUn kwashi mutane da yawa suka tafi da su daji, a yanzu muna jira mu ga me za a yi,” in ji shi.
Rabaran John ya ce ba su iya tantance yawan adadin mutanen da ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su cikin daji ba, “cocin na da mutane da yawa, mutanen da muke zaton an tafi da su sun haura 100.”
A makonnin baya ne gwamnatin jihar Kaduna ta bi sahun jihar Zamfara wajen toshe hanyoyin sadarwa a wasu yankunan jihar a Ć™oĆ™arin da take yi na takura Ć´an fashin dajin tare da shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi jama’a.
Sai dai kuma Rabaran Hayab ya ce har yanzu akwai sauran rina a kaba – saboda duk da matakan rufe hanyoyin sadarwar a wasu yankunan jihar, har yanzu ana ci gaba da sace mutane.
“Matakan ne ba su biya buĆ™ata ba. Kana shan magani ne amma ciwo ya Ć™i warkewa. Dole ne idan za a magance matsalar nan a yi wani abu daban da matakan da ake É—auke a yanzu. Kamar ma mun koma gidan jiya ne.
“Ranar 3 ga watan Oktoba Ć´an bidnga sun shiga wasu Ć™auyuka uku sun kwashi mutum 46. Sannan sun sake zuwa wani Ć™auye shekaranjiya sun kwashi mutum tara da kashe wani mutum guda, kana suna neman mutanen Ć™auyten a yanzu da su ba da kuÉ—i miliyan 50,” a cewarsa.
Kwamishinan harkokin tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya cewa BBC akwai wasu sabbin hare-haren da aka kai wasu yankunan jihar, suna Ć™oĆ™arin tattara duka bayanan, wanda ake sa ran nan gaba kadan a yau za su fitar da sanarwa game da halin da ake ciki da kuma matakan da gwamnatin jihar ke ci gaba da dauka game da matsalolin tsaron da suka addabe ta.

(BBC Hausa)

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...