An kama mata da ta sayar da jaririnta kan ₦500,000

Wata mata mai suna,Chinasa Ukaonu daga jihar Imo ta amsa laifin sayar da jaririnta kan kudi naira dubu ₦500,000.

A cewar rundunar yan sandan jihar,Ukaonu ta amsa laifin nata ne bayan da aka kamata tare da wasu ma’aikatan aikin jinya su biyu da suka taimaka mata wajen sayar da jaririn.

Ma’aikatan jiyar da ake zargi da taimaka mata sun hada da Dorothy Esmonu da Catherine Eke.

Orlando Ikeokwu, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya bayyana cewa matar da ake zargi da sayan jaririn, Chioma Amadi ita ma an kama ta.

Ya ce kama mutanen da ake zargi ya taimaka wajen ceto jaririn.

Ikeokwu ya kara da cewa kwamishinan yan sandan jihar,Rabiu Ladodo ya umarci yan sandan dake binciken batun da su gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...